KOCIYAN GOMBE UNITED YA BAWA YARAN GIDA DAMA

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Gombe United, Manu Garba OON ya bada goron gayyata ga 'yan wasa dake taka Leda anan gida  don gwada sa'ar su.

Cikin wata kebabbiyar zantawa da Manu Garba yace jihar Gombe Allah ya albarkace ta da 'yan kwallo masu basira da hazaka dake taka Leda da kungiyoyi kamar Super Pillars da Flash Flamingoes da Fc Yarmalight da Doma United da Gombe Warriors da Gombe Lions da dai sauran su.
  Ya kara da cewar suna da aniyar surka yaran gida da tsoffin 'yan wasan su na bara hade da gayyatar wasu a wajen jihar mako mai zuwa a shirye shiryen da suke na tunkarar kakar kwallo mai zuwa na NNL

Manu Garba ya yabawa Gwamna Dankwambo saboda jajircewan shi akan kungiyar tare da rokon a sake kudade akan kari don fara shiri da wuri.

Comments