MANU GARBA :BURINA NA MAIDA KULOB DINA PREMIER

   Kociyan Gombe United Manu Garba yace burin shine ya mayar da kulob din zuwa gasar Premier.
    Cikin wata zantawa bayan kulob din ya doke Zaki Mairiga Football Academy a wani wasan sada zumunci, Manu Garba OON ya kara da cewar abinda yasa a gaba shine ganin yadda za'a shirya da wuri don tunkarar gasar NNL.
 Tsohon Kociyan da ya lashe kofin duniya na  ''yan kasa da shekaru 17 ya bayyana gamsuwa da kwazon 'yan wasan shi, amma ya bukace su dasu kara zage damtse.
 Ya bayyana godiyar shi ga Gwamna Dankwambo saboda amincewa dashi tare da cin alwashin zai ba mara da kunya.
  An dai fita hutun rabin sa'a nema da nema, amma sauye -sauyen da yayi ya bawa kulob din nasarar ci hudu da nema, Inda Usman Babalolo ya zazzaga kwallaye uku sai Babagamandi ya zura daya.

Comments