Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya bayyana kaduwar shi visa rasuwar Sarkin Yamaltu,DSP Hassan Usman Jonga mai ritaya.
Cikin wata sanarwa daga kakakin shi ,Ismaila Uba Misilli ,Gwamnab ya bayyana rasuwar basaraken a zaman babban rashi ba ga iyalan sa kawai ba ko masarautar Yamaltu amma ga ilahirin jihar da kasa kwata.
Gwamnan yace marigayin jajirtaccene wanda ya sadaukar da kai wajen yiwa al'ummar shi da jiha da kasa hidima
Ya kara da cewar marigayi DSP Jonga ya taimaka tare da sauran iyayen NASA wajen bada shawarwari don samun zaman lafiya da had in kai da cigaban jiha.
Gwamnan yace a 'yar mu'amalar da yayi da marigayin ya tabbbata mutum nebmai kaunar jama'ar shi tare da son had in kai da cigaban jiha.
Ya kuma jajantawa a madadadin gwamnati da alummar jihar ga masarautar Yamaltu bisa ga wannan babbar rashi tare da addu'ar Allah ya sa aljannar Firdausi makoma.
Comments
Post a Comment