Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya halarci sallar janaza na mahaifiyar Sanata Haruna Garba, Hajiya Hajara ( Jummai) Hassan wadda ta rasu a jiya tana da shekaru 104.
Sallar janazar da akayi a masallacin Jumma'ar Bolari ya samu halartar sanata Danjuma Goje da sarkin Deba da babban hakimin Gombe da wasu manyan mutane.
Tun farko Gamna Inuwa Yahaya cikin wata sanarwa daga kakakin shi ,Ismaila Uba Misilli Ya jajantawa Magayakin Gomben bisa wannan babban rashi na uwa.
Yayi addu'ar Allah ya jikanta ya bawa iyalan hakurin wannan rashi da kuma fatan Aljannat Firdaus ce makoma.
Comments
Post a Comment