Gwamnan Gwambe Ya Halarci Janazar Mahaifiyar Sanata Haruna Garba


Gwamna  Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya halarci sallar janaza na mahaifiyar Sanata Haruna Garba, Hajiya Hajara ( Jummai) Hassan  wadda ta rasu a jiya tana da shekaru 104.

Sallar janazar da akayi a masallacin Jumma'ar  Bolari ya samu halartar  sanata Danjuma Goje da sarkin  Deba da babban hakimin Gombe da wasu manyan mutane.

Tun farko Gamna Inuwa Yahaya  cikin wata sanarwa daga kakakin shi ,Ismaila Uba Misilli Ya jajantawa  Magayakin Gomben bisa wannan babban rashi na uwa.

Yayi addu'ar  Allah ya jikanta ya bawa iyalan hakurin wannan rashi da kuma fatan  Aljannat Firdaus  ce makoma.

Comments