Kungiyar Yan Jarida Ta Kasa Tsangayar Maijalisar Dokoki Ta Tarayya Ta Karrama Kakakin Gwamanan Jihar Gombe
Kugiyar yan Jarida ta kasa Tsangayar maijalisar dokoki ta kasa ta Karrama mai magana da yawun Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na Jihar Gombe,Alh Ismaila Uba Misilli tare da shirya masa kwarya-kwaryar liyafa don taya shi murnar nadin da akayi mashi na babban mai taimakawa Gwamna akan harkokin yada labaru.
Shugabannin kugiyar da Yayanta sun bayyana Ismaila Uba Misilli a zaman jajitacce kuma hazikin dan Jarida wanda suka ji dadin aiki da shi tare da yi mashi fatan alheri a sabon aikin nashi.
Tun farko, Ismaila Uba Misilli ya bayyana farin ciki da wannan karramawa, yana mai cewa bazai taba manta wannan halarci ba.
Kafi nadin nasa, Ismaila Uba Misilli shine Shugaban Kungiyar Yan Jarida ta Kasa (NUJ) Tsangayar Maijalisar Dokoki Ta Kasa.

Comments
Post a Comment