Skip to main content

Kotu Ta Yankewa Maryam Sanda Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

Kotu ta yankewa Maryam Sanda kisa ta hanyar rataya.
Idan ba a manta ba a shekarar 2017 ne rundunar ‘yan sanda da shigar da kara Kotu kan kashe mijinta da wuka da Maryam tayi.
Mijin Maryam, Biyaminu Halliru dan tsohon shugaban jam’iyyar PDP ne Bello Halliru.
Maryam ta musanta cewa ita ce ta kashe, ta bayyana cewa sun kaure da fada ne bayan ta ga wasu hutunan mata sirara a wayar sa. Daga nan ta nemi a yayi mata bayani akai sai suka kaure da fada.
Ta ce a daidai haka ne tulun shishar da ajiye a dakin ya do ya fashe, shi kuma marigayi Bilyaminu ya yanke jiki ya fadi a kai, ya mutu.
Sai dai kuma a binciken da kotu tayi da bayanan da ‘yan sanda suka mika a gaban kotun, ya tabbata cewa wuka ce Maryam ta daba wa Bilyaminu.
Jaridar Premiums Time Hausa tace kotun Mai shari’a Yusuf Halilu, ya kara da cewa wannan bayani da mai kare mai laifi yayi shirya shi aka yi don a yi wa kotu rufa-rufa, amma abin da ya tabbata shine lallai Maryam ce ta daba wa mijinta wuka.

  • Alkalin

Bayan mai shari’a ya yanke hukunci, sai Maryam zabura a guje ta nemi ficewa da ga kotu, sannan ‘yan uwanta suka fara kuwwa suna tsalle da koke-koke.
Daga baya dai da komai ya lafa sai alkali ya ci gaba da karatun hukuncin sa.

Comments