Bikin Wasanni Na Ƙasa: Hukumar Wasanni Na Jihar Gombe Ta Shigar Da Masu Motsa Jiki Sansanin Ƙarɓan Horo



Kimanin masu wasannin motsa jiki 142 ne da zasu wakilci jihar Gombe a bikin wasannin kasa karo na ashirin suka fara keɓaɓɓen sansanin karbar horo na kwanaki goma.

Shugaban hukumar wasanni  Executivena jihar Gombe, Alhaji Hamza Adamu Soye ne ya sanar da hakan a lokacin da yake ganawa da masu rubuta labarin wasanni game da yadda jihar ta shirya wa bikin a ofishin.


Alhaji Hamza Adamu Soye yace hukumar ta kammala dukkan shirye-shirye don samun nasarar horon inda ya buƙace su da su maida hankali a horon da za'a basu wurjanjan a tsawon wannan lokaci.

Jami'an gudanar da harkokin wasannin Theya yaba wa Gwamna Inuwa Yahaya bisa tallafin kuɗi da yake basu ba gajiyawa wanda hakan ya bada nasarar da aka samu zuwa yanzu inda ya tabbatar da cewar zasu yi iyakar ƙoƙarin su wajen lashe lambobin yabo.
 A cewar shi jihar Gombe zata fafata a wasanni goma sha huɗu daga cikin talatin da ɗaya da cikin su akwai ƙwallon kwando da na hannu da na raga na bakin kogi da ma ɗaiɗaikun wasa.

Ya bayyana cewar jihar ba yawon buɗe ido zata birnin Benin ba amma da zimmar lashe lambobin yabo duk kuwa da mai masaukin baƙi da wasu jihohi sun yi zarra a harkar.

Tawagar mutane 194  da ta ƙunshi jami'ai da masu horar wa da ƴan wasa zasu bar jihar Gombe zuwa Benin a ranar 20 ga watan Maris yayin za'a fara bikin wasannin motsa jiki na ƙasar daga ranar 22 ga watan Maris zuwa 2 ga watan Afrilu

Comments