Covid-19: Kamfanin Siminti Na Ashaka Ya Gwangwaje Gwamnatin Gombe Da Cibiyar Keɓe Masu Corona



Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya yabawa kamfanin siminti na Ashaka, wadda reshe ne na Kamfanin Lafarge Africa, bisa dafawa yunkurin Gwamnatin Jihar Gombe na magance yaduwar annobar COVID-19, inda ya bada tallafin cibiyar kebe masu fama da cutar dauke da cikakkun kayan aiki dama wassu ababen da dama.

Da yake jawabi yayin mika cibiyar da kamfanin yayi a hukumance ga gwamnatin jihar a garin Ashaka, gwamna Inuwa wadda ya samu wakilcin mataimainsa Dr. Manassah Daniel Jatau, yace tallafin cibiyar da sauran kayan aiki zasu taimaka gaya wajen takaita illar cutar.

Yace annobar wacce ta zama alakakai ga duniya baki daya sai anyi mata taron dangi, yana mai kira ga sauran kungiyoyi da daidaikun jama’a da suma su bada tasu gudunmowa wajen yaki da cutar.

Yace kamfanin na Ashaka ya nuna karamci abun koyi da zai yi tasiri a rayuwar al’ummah dama na baya masu tasowa, yana mai kira ga sauran kamfanoni dake jihar dasuyi koyi da wannan karamci na kamfanin Ashaka.

Sai ya bayyana fargaba ganin yadda annobar take kara kamari, bisa la’akari da rahotanni na baya-bayan nan dake nuni da yadda cutar ke rubanya ninkin ba ninki, yana mai jaddada bukatar koya ya cigaba da dabbaka matakan kariya na wanke hanu akai-akai da gujewa cunkoso da amfani da kyallen rufe baki da hanci da kuma zama a gida.

Gwamnan yace lamarin cutar a Gombe yasha bamban ganin yadda aka samu kimanin mutane 30 da suka kamu da ita cikin kasa da mako guda, amma yace hakan na nuni da irin azamar da kwamitin kar ta kwana kan yaki da cutar yayi na gano masu cutar da wuri kafin su cakudu da sauran jama’a.

Ya kara da cewa gano masu cutar da akayi wata alama ce dake nuni da cewa kwamitin ba kawai ya takaita ga masu dauke da cutar bane, amma har da kokarin gano wadanda suka mu’amalancesu.

Da yake mika cibiyar ga gwamnatin jihar, manajan daraktan kamfanin simintin na Ashaka Ibrahim Aminu, yace tallafin wani bangare ne na sauke nauyin hidimtawa al’ummah dake kan kamfanin ta fuskar dafawa gwamnati wajen yaki da annobar.

Yace cibiyar mai gadaje 12 tana dauke da muhimman kayayyakin jinya da ake bukata don kula da wadanda ake zargi ko aka tabbatar sun kamu da cutar.

Manajan ya kara da cewa kamfanin ya kuma bada tallafin sinadarin kashe kwayoyin cuta na sanitizer guda 120 da samar da fotuna da takardun fadakarwa da wayar da kan jama’a cikin harshen Hausa.

Da yake bayyana kwarin gwiwar cewa tallafawa gwamnatin zai taimaka wajen ganin bayan yaduwar cutar, Ibrahim Aminu yace kamfanin ya kuma sayo motar daukan marassa lafiya da ake kira ‘‘ambulance’’ dauke da cikakkun kayan aiki don karfafa shirin gwamnatin jihar na kota kwana.

Yace sauran kayayyakin tallafin kamar kyallen rufe baki da hanci da sauran na kare kai na nan tafe bada jimawa ba don mikasu ga kwamitin.

Ibrahim Aminu wadda ya zagaya da jami’an gwamnatin jihar ciki da wajen cibiyar, yace uwar kamfanin na Lafarge Africa ya shirya samar da tallafin kayan abinci ga kimanin magidanta dubu 3 a yankin don rage musu radadi.

Shugaban kwamitin aiki da cikawa kan yaki da cutar Parfesa Idris Mohammed, ya mika godiya da yabawa kamfanin bisa wannan tallafi, yana mai bada tabbacin yin amfani da cibiyar da sauran kayayyakin yadda ya dace.

Ismaila Uba Misilli

Babban mai taimakawa gwamna na musamman kan yada labaru da hulda da yan jaridu

Comments