Gwamnan Jihar Gombe
Muhammadu inuwa Yahaya ya bayyana kaduwa da jimaminsa game da rasuwar shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Malam Abba Kyari, wadda ya rasu jiya Juma'a.
Gwamna Inuwa Yahaya yace tabbas Najeriya tayi rashin haziki mai kishi kuma kwararre a sha'anin mulki wadda kullum baya wasa da aikinsa.
Yace za'a cigaba da tunawa da tsohon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar bisa irin jajircewansa, da sadaukarwa da biyayya a yayin gudanar da ayyukansa.
Gwamnan yace "A madadin gwamnati da al'ummar Jihar Gombe, ina mika jaje da ta'aziyya ga shugaban kasa da iyalan marigayin dama gwamnati da al'ummar jihar Borno bisa wannan babban rashi."
Gwamnan na Gombe sai yayi addu'ar Allah ya jikan marigayin yasa Aljannah Firdausi ce makomarsa ya kuma bawa iyalansa hakurin jure wannan rashin.
Ismaila Uba Misilli
Babban mai taimakawa gwamna na musamman kan yada labaru da hulda da yan jaridu
Comments
Post a Comment