A Ceci Rai: Jamilu Abdullahi Yana Nemar Gudumawar Naira Dubu 800 Don Yi Ma shi Tiyata

Jamilu Abdullahi, Matashi ne mai hazaka da ya ke neman na kansa wanda hakan ta sa yake rike da akalar gidan su , wajen dawainiyar yau da kullum ta Mahaifi da mahaifiyar sa da sauran 'yan uwansa Maza da mata.

Sai dai cikin hukuncin Allah , Jamilu ya gamu da lalura data kai ga kwantar da shi tare da yi masa aikin tiyata (Operation ), wanda hakan tasa ba a fita nema, kuma dan abinda ake dashi duk ya tafi a wajen lura da lafiya da siyen magani ,wanda hakan ba karamin jefa iyayen sa da 'yan uwansa cikin halin kaka nikayi ya yi ba.

A binciken da aka gudanar da gwaje -gwaje a Asibitin Malam Aminu Kano, an gano cewar matashi Jamilu wanda ake wa lakabi da 'Saso', na fama da lalurorin da suka hada da.

1)Cutar Daji wato (Cancer ) wacce a yanzu haka ta sake tsirowa tare da mamayar ilahirin kayan cikin sa.

2) Ciwon Koda .

3) Da ciwon Hanta.

Hakan ta sa aka rubuta masa ,kudin gudanar da sabon aiki na tiyata (Operation ) da kuma kudin allurori da magunguna da zai amfani dasu bayan gudanar da aikin da suka kama , naira dubu dari takwas , 800, 000, wanda yanzu haka maganar da muke Jamilu da ahalin su basu da wannan kudade , ta abincin da za aci ma ake  fafutuka saboda yanayi  na rayuwa.

Zuwa yanzu haka lokacin da aka dibar masa na lokacin yin aiki ya wuce tun ranar 24 ga watan Afrilun daya gabata na shekarar 2020, wanda likitan dake duba shi yace ,da zarar lokacin ya wuce zai fuskanci matsalolin, rashin yin bayan gida, Firsari, Kumburin jiki, da kuma rubewar Ciki, wanda a halin yanzu halin da matashi Jamilu ke ciki ke nan.

Hakan ta sa  Jamilu , na neman gudunmowar ki /ka, a wannan hali da yake ciki kasancewar bashi da yadda zai yi, don samu a gudanar da aikin tare da taimakon lafiyar matashin ,da fatan za mu taimaka don ceto shi daga halin da yake ciki , Allah ya bamu ikon taimakawa da kuma ladan taimakon ,shi kuma ya bashi Lafiya Amin s Amin.

Ga duk mai son taimakawa, zai iya bada gudunmowar sa a Asusun (Accounts )da aka ware kamar haka....

1- Bank :FCMB
     Account name :Nassarawa Equal development advocates .
     Account :6427681010.

2- Bank :First bank
    Account name :Aminu Halilu Tudunwada.
    Account :3090477839.

3- Acc Name_ Bridge Nigeria Initiative
     Acc Number_ 0041523760
     Bank_ Unity Bank

Allah ya sa mu dace ya iya mana Amin !!

08067320041
08033976354

Comments