Ƙaramar Sallah: Gwamnan Gombe Ya Taya Al'ummar Musulmi Murna



Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, ya taya al'ummar Musulmin jihar da takwarorinsu na duniya murnar sallar Eidul fitr dake alamta kammaluwar azumin watan Ramadan cikin nasara.

Ta cikin wani sakon taya murna da barka da sallah, gwamnan ya bukaci Musulman dasu cigaba da dabbaka darusan da suka koya a wata mai alfarma na Ramadana a sauran kwanaki na rayuwarsu.

Yace "Bikin sallar na koyar da sadaukarwa da taimako da nuna kauna ga juna da biyayya ga koyarwar addinin Musulunci. Don haka ina kira a garemu da mu dauki darasi daga watan na Ramadan kuma mu nuna kauna da soyayya ga juna dama yaukaka zaman lafiya da fahimtar juna a tsakaninmu al'ummominmu mabanbanta."

Ya kara da cewa "Kamar yadda muka yi ta tunawa da marassa karfi da talakawa da marassa lafiya a wannan wata, ina kira a gare mu da mu cigaba da dabbaka su har bayan Ramadan."

Da yake kira ga sarakuna da malaman addini da shugabannin al'ummah dasu cigaba da ririta zaman lafiya da tsaron da ake dashi don cigaban zamanta kewa dana tattalin arziki, Gwamna Inuwa ya bada tabbacin gwamnatinsa na cigaba da samar da ayyukan cigaba don nausa jihar gaba.

Gwamnan sai ya jinjinawa al'ummar Musulmi da sauran jama'ar jihar bisa hakurin da suke nunawa a wannan lokaci mai cike da kalubale da matsalolin da annobar coronavirus ta haifar, yana mai kira garesu dasu cigaba da addu'a da bawa gwamnati hadin kai da goyon baya wajen yaki da cutar.

Yace "Ina kuma kira a gareku da ku cigaba da dafawa kokarin gwamnati kan yaki da mummunar cutar ta Covid-19, ta hanyar daukan matakan  kare kai da biyayya da dokokin takaita zirga-zirga, ina kuma baku tabbacin cigaba da himmatuwar mu na daukan matakan dakile cigaba da yaduwar cutar a jihar mu."

Gwamna Inuwa sai ya bada tabbacin gwamnati na yin duk abinda ya dace na tabbatar da zaman lafiya da walwalar al'ummar jihar.

Ismaila Uba Misilli
Babban mai taimakawa gwamna na musamman kan yada labaru da hulda da jama'a

Comments