Ranar Yanjarida Ta Duniya: Gwamnan Gombe Yayi Jinjina Ga Yanjarida Bisa Rawar Da Suke Takawa Wajen Yaki Da Cutar Corona




Yayinda yan jaridu a Jihar Gombe suka bi sahun takwarorinsu na duniya don bikin ranar yancin yan jaridu ta duniya ta bana, Gwamnan jihar Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya jinjinawa ma'aikatan kafafen yada labarai a jijar bisa jajircewa da himmatuwarsu na fadakarwa da wayar da kan yan kasa game da shirye-shirye da manufofin gwamnati dama harkokin cigaban duniya a daidai lokacin da ake fama da annobar coronavirus.

A wani sakon fatan alheri, Gwamna Inuwa ya yaba da irin sadaukarwa da hobbasar yan jaridu a Jihar Gombe game da yadda suke bada rahotanni kan annobar Covid-19, dama yadda suke wayar da kan jama'a kan biyayya da dokar takaita zirga-zirga da dabbaka matakan kariya daga annobar.

Da yake tsokaci kan taken ranar ta bana wato "Aikin jarida ba tare da tsoro ko son rai ba" gwamnan yace a matsayin masu sanya ido kan al'ummah kuma muryar jama'a, dole ne yan jaridu su cigaba da dabbaka dokokin aikinsu ta hanyar yayata muradun demokradiyya da adalci da daidaito, da zaman lafiya da hadin kai dama cigaba da sanar da jama'a kan harkokin cigaba a duniya ta cikin rahotanni da sharhin su.

Da yake bukatar ma'aikatan na kafafen yada labarai da suyi kaffa-kaffa da yada labarun karya dana bogi dama tabbatar da gaskiya da daidaito a rahotannin su, Gwamna Inuwa ya bada tabbacin cigaba da aiki dasu a matsayin muhimman abokan cigaba, a kokarinsa na tabbatar da shugabanci na gaskiya da adalci a Jihar Gombe.

Ismaila Uba Misilli
Babban mai taimakawa gwamna na musamman kan yada labarai da hulda da yan jaridu

Comments