Gwamna Ganduje Ya Yabawa Mu'azzam Bisa Rawar Da Yake Takawa A Matsayin Mai Bada Shawara Na Musamman Akan Harkokin Wasanni

Mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Kano kan harkokin wasanni Alhaji Ibrahim Mu’azzam Madaki ya jagoranci tagawar kungiyoyin kwallon na jihar Kano a wajen bikin ranar matasa ta duniya, wanda ma’aikatar matasa da wasanni ta jihar Kano karkashin jagorancin Comrade Kabiru Ado Lakwaya ta shirya, inda aka gudanar da taron a filin wasa na Sani Abatcha dake Kofar Mata.

Taron ya samu halartar mai girma gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Mataimakin sa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da kwamishinoni da sauran manyan jami’an gwamnati.

Haka kuma, mai girma gwamna ya yabawa Alhaji Ibrahim Mu’azzam Madaki dangane da yadda ya shirya tagawar ‘yan kwallon kafa da suka halarci taron.

Comments