Hukumar Ilimin Bai Ɗaya Ta Jihar Gombe SUBEB Ta Shiryawa Shugabannin Makarantu Da Malamai Taron Bita

Daga Sani Sabo

Da safiyar yau laraba 30/9/2020 hukumar Ilimin bai daya na 'SUBEB' karkashin jagorancin shugaban hukumar Mr. Babaji Babadidi ta jagoranci wani kwaryakwaryan karawa juna sani dan shirye-shiryen sake bude makarantu a matakin farko.

Yakuma gudana ne a Kolejin Ilimi na gwamnatin tarayya 'Federal college of education technical Gombe' ya samu halartan Kodinetan hukumar Ilimin bai daya na kasa 'UBEC' dake Arewa maso gabas, Mambobi a hukumar Ilimin bai daya na jaha 'SUBEB' Prof. Shuaibu Umar Doho mamba I, Dr. Abubakar Abdullahi Kumo mamba II, Mallam Sani Sabo mamba III, shugabannin makarantu da sauran malamai a fadin jahar.

Wannan yana daya daga cikin shirye-shiryen kara bude makarantu a fadin jahar wanda ya samu tseko a watannin baya, sanadin korona da ya addabi tattalin arzikin duniya (Global pandemic).

Muna addu'ar Allah yasa a bude cikin nasara...

Comments